Saturday, January 14, 2012

Cire tallafin man fetur Gwamnati ba ta wakiltar al�umma: Sheikh Ibrahim Zakzaky

Mai karatu wannan wata tattaunawa ce da Sayyid Ibraheem Zakzaky ya yi da gidan talabijin na jihar Kebbi, Kebbi TV, a lokacin da ya je jihar domin rufe taron Mu�utamar Amm da aka gudanar a garin Birnin Kebbi a ranar Asabar da ta gabata. An yi wannan tattauanawa ce a masaukin da Sayyid ya sauka. A cikin wannan tattaunawar, Sayyid Zakzaky ya fara ne da bayyana dalilan zuwansa Birnin Kebbi. Ya kuma yi tilawar abubuwan da suka faru a lokacin batun shari�ar Zamfara da wasu jihohi a shekarun baya. Haka kuma Sayyid Zakzaky ya yi cikakken bayani game da halin da ake ciki na janye tallafin man fetur, matakin da �yan kungiyar kwadago suka dauka da kuma mafita ga wannan al�amari. Kada dai mu cika ku da surutu, Musa Muhammad Awwal na nan a lokacin wannan tattaunawar, kuma ga cikakkiyar hirar nan kamar yadda ya rubuto mana.

KEBBI TV: Ko za mu san abin da ya kawo Malam zuwa jihar Kebbi?

SAYYID IBRAHEEM: Bismillahir rahmanir rahim. Akwai wani taro da ake ce ma na kara ma juna sani wanda su ba�adin �yan uwa suka shirya a nan Birnin Kabbi na kwana uku, wanda ya fara daga Juma�a ya kare a yau Lahadi. To, ni an gayyace ni ne domin in zo in yi jawabin rufe shi taron. Sai su kuma �yan uwa din suka dauki wannan dama ta zuwa rufe wannan taro din suka shirya wadansu abubuwa, wadanda suka hada har da wa�azi da aka yi ma al�umma gaba daya a jiya da daddare, da kuma wadansu �yan ziyarori da za a yi. Muna iya cewa har da wannan inta-biyu taku. Amma makasudin zuwan shi ne wannan rufe taro din.

KEBBI TV: A shekarun baya �yan siysa sun kaddamar da abin da suke ce ma jaddada shari�a a wasu jihohin kasar nan. Allah gafarta Malam, Shari�ar nan ta amfani wadanda aka yi dominsu?

SAYYID ZAKZAKY: To, na farko dai su �yan siyasa din sun sa siyasa a cikin al�amarin. Maimakon in da ikhlasi suka so yin abin, sai su fadi takamaimai abin da suka so su yi. Da sun ce za a kawo gyara a tsarin shari�a na jiha ta yadda za a kara fadin shari�ar Musuluncin daga tsukakken abin, da kula da abin da ya shafi iyali, da rabon gado da aure, a fadada shi ya zuwa sauran laifuffuka masalan, to da mutane sun fahimci abin kuma cikin sauki. To, amma sai suka fadada abin, suka ce za a zo da shari�ar Musulunci, wato jihar ma gaba daya za ta koma ta shari�a ne.

To, su kuma mutane da suka ji wannan sun dauka yanzu kamar za a koma abin da dama aka gada ne, za a kawar da abin da Bature ya kafa mana kenan. Domin Bature ya zo ya same mu muna nizamin shari�a ne. To sai, mutane suka dauka irin wannan za a koma. Har akwai jaridar da ta rubuta bangajeje a shafinta na farko, ta ce �Islamic State of Zamfara�. Haka wannan wata jarida, TRUST ta rubuta. Wato ita abin da ta fahimta za a koma a yi kasar Musulunci ne da tsari irin na Musulunci. To, a karshe sai ta zamana ba wani abu aka yi ba illa shari�ar da dama akwai ta, tana nan, da kotunan da dama suke nan, su ne aka yi masu �yan kwaskwarima, aka gyaggyara kotuna, aka giggina �yan sababbi, aka dan kwakkwafa albashi na ma�aikata, shi kenan. Ka ga da tun farko�tunda a aikace dai abin da muka ga sun yi kenan, an dan yi kwaskwarima ne. To, da tun farko in ka zo ka ce za ka yi kwaskwarima, ai ba wanda zai tsammaci wani abu.

Kamar yadda nake cewa, in da mutum zai zo ya ce zai gyara gari, ya yi sababbin tituna, ya gyaggyara tsofaffi, ya yi hanyoyin ruwa, ya sa fitillu da sauransu, ya ce za mu gyara gari, ka ga za mu san abin da yake nufi, sai ya ce za mu gina sababbin garuruwa. To sai a karshe kawai muka ga ya dan yi �yan gyare-gyare ne. Ka ga in ka ce za ka gina sabon gari, za mu dauka za ka share wani daji ne ka gina gidaje ka fid da komai da komai, ka ce ga sabon gari na gina ko? To haka suka yi mana. Sai suka ce za su yi shari�a ne, sai mutane na tsammanin abin da za a yi kenan, sai suka karata a gyara. To, da sun ce gyaran za mu yi, to da ma ba za a damu ba. Amma muna tsammanin sun fadi wannan ne domin ya amfane su a siyasance, ya ba su farin jini da suna a siyasance, amma karshe dai abin da suka yi kenan.

KEBBI TV: Allah ya gafarta Malam akwai fitintinu da suka kunno mana kai yanzu a wannan kasa. A taka fahimtar, me kake jin ya kawo wannan abu, kuma ina ne mafita?

SAYYID ZAKZAKY: To, shi nizamin da ke iko, shi yana da muradi, yana amfana da wadannan rigingimun, don haka shi ke haddasawa. Wannan wani abu ne wanda wadanda suka yi karatun sha�anin zaman dan Adam suka sani, kamar wadanda suka karanta sha�anin �Sociology� da ma �Political Science� za su iya sanin cewa galiba nizami yakan kirkiro da fitinu don ya amfana da su. Mun ga wannan a zaben da aka yi baya, shi nizamin ya amfana da rigimar da ta biyo bayan zabe din, kuma shi ya haddasa rigimar. Domin sai aka daina maganar sakamakon zabe, aka koma ana kokari a zauna lafiya. Ka ga ko ka ci zabe ko ba ka ci ba, yanzu dai ka ci, tunda yake yanzu ba maganar zaben ake ba, ana batun a zauna lafiya ne. To, ka ga sun amfana da wannan ta wajen an manta da ba su suka ci zabe ba, amma an danna su. Ban ce ba kowa ne bai ci zabe ba, akwai wadanda suka ci, akwai wadanda ba su ci ba, amma wa ke maganar wadanda ba su ci ba? Duk an ci aka zauna, to ka ga rigima ta amfane su. Shi ne nake cewa sun yi siyasa da jinainan mutane. Amma kar su dauka za su wuce da shi, don sakamakon zai biyo baya a nan (duniya) da can (lahira).

Sannan abu na biyu kuma, ka ga kamar wannan rigimar da suke saka mutane a halin zaman dar-dar da zaman tsoro, yadda ya zama yanzu kowa a tsorace yake, a gida yake ko a waje, ana ta ta da bama-bamai. Kuma yanzu ma sai suka yi ta munana, suna nufatar wuraren ibada na mutane, wato suna neman su haddasa fitina tsakanin addinai daban-daban. Ko da gani nizamin su ne da abinsu. Domin ba za mu iya gane wai a ce akwai wasu mutane wai suna da wata da�awa da wata manufa ko ma mecece manufar tasu, amma ya zama ba a ji maganarsu ba, ba a san su ba, ba a ji komai daga gare su ba, sai kawai a ji bom ya tashi. To wace nasara za su cimma wajen kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba? Kuma a ce wadannan mutanen sunansu kawai ake ji, an kala masu wani suna, amma ba za ka iya nuna mani ko mutum daya ba, yana wucewa ka ce ka ga wancan, ai dan Boko haram ne. Ko kuma kana tafiya ka ce ka ga masallacin nan na Boko Haram ne, ko ka ce mani ka ga jaridar Boko Haram, ko ka ga adires din Boko Haram, ko ka ga lambar wayar �yan Boko Haram, ba ko guda, sai kawai bom ke tashi.

To, muna ganin wannan ba wani aiki ba ne illa aikin nizamin da ke iko, musamman ma da ya gayyato Amerika ya ce ya ba shi tsaro. Tunda yake ya sami kwangila mai tsoka wajen ba da tsaro, to dole kuwa ta haddasa wadansu abubuwan da zai nuna tana aiki, saboda haka ita za ta haddasa fitinar ta ce tana magance shi. Har yanzu ban ji wani wanda ya yi tambaya ba, ya dauko baraguzan bom din da ke tashi ya ce wane irin bom ne, a ina aka yi shi? Ana sayar da shi a kasuwa ne, ko kuwa irin na soja ne? Ba wanda ya tambaya, sai kawai a ce wai wani abu wai shi Boko Haram ne ya yi. Su ne suke sa wa. Na karanta a intanet wani Ba�amerike ya rubuta yake cewa bama-baman da suke tashi, wadanda aka gayyato su yi maganin abin, su suka yi bom din. Wannan Ba�amerike ke fadi. Su suke sa wa, kuma su ba da tsaro. Kuma wannan ba bakon abu bane, sun yi a wasu wurare, sun yi a Irak, sun yi a Afghanistan da Pakistan da kasashe daban-daban. Sun je da manufar mamaye kasar da dibar dukiyar da rarraba su. To, kuma suna da wannan manufar a Nijeriya, na cewa suna so su zo su mamaye wannan kasar, za su zo ne da sunan kawo zaman lafiya, sai su mamaye, su dibi dukiya su raba kasa din, suna da niyyar raba kasar. Sai dai rabuwar, a nasu tunanin sun dauka Nijeriya ta rabu zuwa Kudu da Arewa ne, Arewa Musulmi, Kudu Kirista, haka suka dauka, kuma za su raba ta biyu ne. KEBBI TV: A karshe, akwai batun janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi, kuma da shiga yajin aiki da kungiyar kwadago ta yi. A matsayinka na masani, me za ka ce, kuma menene mafita?

SAYYID ZAKZAKY: To, ko ba komai wannan ya nuna maka yanzu muna da gwamnati, wadda ba mu take wakilta ba, ba mu take ma aiki ba, ba ta ma damu da mu ba, domin suna janye tallafin, sai ga gwamnatin Amerika ta taya su murna, to ka ga ita ta sa su kenan. Banda haka ba ya za a yi a ce gwamnatin al�umma ta mutane ta kuntata masu, ta dadada ma wani na waje? Ka ga yanzu wani al�amari ne da ya nuna cewa hukumomin na wasu ne, su suka sa su, kuma suna masu aiki, ba al�umma ta dame su ba. Domin wanda duk ya dage tallafin mai, ba masoyin kasarsa bane, makiyinsu ne, domin in mai ya yi tsada komai zai yi tsada, komai na rayuwar mutane. Kuma a karshe talaka ne zai ci muguwar wahala.

Abin yi, ya kamata al�umma su san cewa wannan ba wani abu ne wanda za su zura ido su ce wata ko kungiyar kwadago za ta yi ba, gaba dayan al�umma ne ya kamata su ce in dai don mu ne ake (cire tallafin), to mu ba mu bukata. Suna kawo hujjar cewa wai kudi za su samu su yi wasu ayyuka, to in da gaske ne suna son yin ayyukan ne, sai a ga sun nemi wadansu dibarori na yin ayyuka, ba dibarar kuntata ma mutane ba. Kamar mutum yana fama da rashin lafiya za ka ba shi magani, ko kuma yana fama da yunwa, za ka ba shi abinci, sai kuma ka ce amma za ka yi hakuri sai na kwakule maka ido kafin in ba ka tuwo, an ba ka tuwo ka ci kuma an cire maka ido, ko hakori. Ai kamata ya yi ya san dibarar da zai yi ya ba ka lafiya ya ba ka abin ci, ba ya zo ya cutar da kai ta wani bangare ya ce ya kyautata maka ta wani bangare ba. Kamata ya yi in da da gaske ne suna so su taimaki al�umma ne, su yi tunanin yadda za su taimaki al�umma din ba yadda za su kuntata masu ba. Amma yanzu fi�ilan sun kuntata ma mutane ne. To, kuma al�umma ne ya kamata su fahimci wannan, kar su saki abin ga kungiyar kwadago kawai, don kungiyar kwadagon ma, mu ba amince masu muka yi ba, ana nan ana iya sayen manyansu, sai daga baya su ce sun yi sassauci, sun janye, shi kenan zance ya kare, bayan abu ya zo. Ya kamata al�umma ne su ce su dai kam in dai su ake yi ma, to ba su bukatar dauke tallafin.

KEBBI TV: Akramakallah mun gode.

SAYYID ZAKZAKY: To, masha Allah.